Rahotanni sun ce an kashe mutane uku bayan wasu ’yan bindiga sun kai hari wurin haƙar ma’adinai da ke garin Jol, ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin Talata, lokacin da maharan suka kutsa wurin tare da buɗe wuta kan mutanen da ke wajen.
Wani mazaunin yankin, Bulus Shen, ya tabbatar da harin, inda ya ce lamarin ya jefa al’umma cikin fargaba. Kakakin ƙungiyar Berom Youth Moulders Association, Rwang Tengwong, shi ma ya tabbatar da faruwar harin tare da yin Allah-wadai da kisan.
Tengwong ya buƙaci jami’an tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa, su kama waɗanda suka aikata laifin tare da ƙarfafa tsaro a yankunan karkara. Sai dai ’yan sanda da Operation Enduring Peace ba su mayar da martani kan lamarin ba.
Harin ya zo ne kwanaki biyu bayan kashe mutane biyar, ciki har da soja, a Barkin Ladi. Duk da dokar hana fita da gwamnatin Plateau ta sanya tun ranar 21 ga Satumba, ana ci gaba da samun hare-hare a wasu sassan jihar.