Saturday, November 7, 2026
HomeLabaraiTinubu ya isa Akwa Ibom domin ƙaddamar da ayyuka da halartar gangamin...

Tinubu ya isa Akwa Ibom domin ƙaddamar da ayyuka da halartar gangamin APC

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa birnin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, domin ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Gwamna Umo Eno ta kammala, tare da halartar gangamin jam’iyyar APC.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya isa birnin Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom, domin ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Gwamna Umo Eno ta kammala, tare da halartar gangamin jam’iyyar APC.

Tinubu ya isa jihar ne a ranar Juma’a, a matsayin wani ɓangare na ziyarar aiki da zai kai jihohin Akwa Ibom da Rivers. Wannan ne babban rangadin farko da ya kai yankin Kudu maso Kudu tun bayan fara shirye-shiryen APC gabanin zaɓen 2027.

Gwamna Umo Eno, jami’an gwamnati, shugabannin APC da magoya bayan jam’iyyar ne suka tarbe shi a filin jirgin saman Victor Attah da ke Uyo.

A yayin ziyarar, ana sa ran Tinubu zai ƙaddamar da sabon ginin tashar jiragen sama ta ƙasa da ƙasa, asibitin filin jirgin da kuma Ibom Aviation Village.

Sauran ayyukan sun haɗa da hanyar Airport-Okopedi, Ring Road 3, ginin ofishin AKWA-GIS, cibiyar sa ido da kula da tsaro ta Command and Control Centre, da kuma ARISE Palm Resort.

Bayan ƙaddamar da ayyukan, ana sa ran shugaban ƙasar zai halarci gangamin APC a filin wasa na Godswill Akpabio International Stadium da ke Uyo.

SourceVanguard
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments