Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiSarki Sanusi II ya gargaɗi gwamnati kan kallon masu sukarta a matsayin...

Sarki Sanusi II ya gargaɗi gwamnati kan kallon masu sukarta a matsayin makiya

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargaɗi gwamnatin tarayya da ta guji kallon mutanen da ke sukar manufofinta a matsayin makiyan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa ya kamata gwamnati ta riƙa karɓar suka mai ma’ana domin gyara kura-kurenta.

Sanusi ya bayyana hakan ne yayin wani taron shugabanci na Oxford Global Think Tank Leadership Conference da aka gudanar ta yanar gizo a ranar Talata.

Ya ce bai kamata gwamnati ta ɗauki korafe-korafen jama’a kan talauci da tsadar rayuwa a matsayin ƙiyayya ko suka gare ta ba, musamman ganin yadda al’umma ke fuskantar matsin tattalin arziki.

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kuma nuna damuwa kan yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, yana mai cewa ya kamata Najeriya ta tsara abubuwan da za ta ba fifiko, musamman a fannonin hanyoyi, wutar lantarki, noma da fasaha.

Sanusi ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun haifar da wasu ci gaba, inda ya bayyana cewa haɓakar tattalin arziki ta tashi daga kashi 0.9 zuwa 4.5, yayin da hauhawar farashi ta ragu daga sama da kashi 30 zuwa 14.5.

Sai dai ya ce duk da waɗannan nasarori, har yanzu akwai manyan ƙalubale da suka haɗa da talauci, yunwa, ƙarancin abinci mai gina jiki, mace-macen mata masu juna biyu da matsalolin ilimi da lafiya.

Sarkin ya kuma bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar waje ta Babban Bankin Najeriya ta kai dala biliyan 55, amma hakan bai kawar da matsalolin da talakawa ke fuskanta ba.

Ya buƙaci gwamnati ta magance matsalar ɗorewar bashin ƙasa, tare da samar da tallafin rage raɗaɗin sauye-sauyen tattalin arziki ga talakawa tun daga farkon aiwatar da su.

Sanusi ya ƙara da cewa bai kamata gyaran tattalin arziki ya tsaya kan cire tallafin man fetur da sassauta farashin canjin kuɗi kawai ba, yana mai cewa akwai buƙatar yin garambawul a sauran fannoni domin sauye-sauyen su amfani jama’a.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments