Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 16 ga Janairu, 2027, bisa la’akari da yanayin siyasar ƙasar.
Barau ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓe na ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a jihar Kano, inda ya buƙaci ’yan APC su yi aiki tukuru domin samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya ce matakan da Tinubu ya ɗauka a wa’adinsa na farko za su haifar da sakamako mai kyau a wa’adinsa na biyu. Ya kuma gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran shugabannin jam’iyyar bisa goyon bayan da suke bai wa APC.
Barau ya bayyana Kano a matsayin muhimmiyar jiha saboda yawan masu rajistar zaɓe, yana mai cewa komawar Gwamna Abba daga NNPP zuwa APC ta ƙara wa jihar muhimmancin siyasa tare da buɗe damar samun ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya.
Ya ƙara da cewa haɗin kan shugabannin APC a Kano, ciki har da gwamnati, ’yan majalisu da shugabannin ƙananan hukumomi, zai taimaka wajen samun nasarar jam’iyyar da kuma kawo ci gaba ga al’umma.