Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiNELFUND za ta dakatar da tallafin kuɗin karatu ga ɗaliban da iyayensu...

NELFUND za ta dakatar da tallafin kuɗin karatu ga ɗaliban da iyayensu ke ɗaukar nauyinsu

Asusun ba da lamunin kuɗin karatu na Nijeriya (NELFUND) ya bayyana shirin ɗaukar matakan dakatar da tallafin lamunin karatu ga ɗaliban da ke cin gajiyarsa, duk da cewa iyayensu na ci gaba da biyan musu kuɗin makaranta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Manajan Daraktan NELFUND, Akintunde Sawyerr, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba.

Sawyerr ya ce asusun ya gano wasu ɗalibai da ake zargin suna karɓar lamunin kuɗin karatu, alhali iyayensu na ci gaba da biyan kuɗin makaranta da sauran buƙatunsu na karatu.

Ya ƙara da cewa NELFUND na nazarin wannan lamari domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga ɗaliban da suke da buƙatarsa da gaske, tare da hana waɗanda ba su cancanta ba ci gaba da cin gajiyarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments