Shugaban ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, Nura Umar Abdullahi, da wasu mutane huɗu da aka yi garkuwa da su sun samu ’yanci bayan sun tsere daga hannun ‘yan ta’adda.
Mutanen sun tsere ne da safiyar Alhamis, 24 ga Satumba, a yankin ƙaramar hukumar Kaura Namoda, yayin da dakarun Operation FANSAN YAMMA ke gudanar da samamen leƙen asiri kan wata maboyar ‘yan ta’adda.
Bayan tserewarsu, dakarun sojin sun karɓe su tare da ba su kariya, kafin a kai su wani asibitin soji domin kula da lafiyarsu da gudanar da gwaje-gwaje da tambayoyi na yau da kullum.
Nura Umar Abdullahi ya shafe kusan kwanaki 61 a hannun masu garkuwa da mutane, bayan da aka sace shi daga gidansa da ke Bungudu a watan Yulin 2026.
Rundunar sojin ta ce a riga an mayar da ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ga iyalinsa, yayin da ake shirye-shiryen haɗa sauran da iyalansu.