Kwamishinan Ƴan sandan Jihar Benue, Cletus Nwadiogbu, ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da cafke sauran mutanen da ake zargi suna da hannu wajen kai hari ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi.
Ya ce rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an gano duk waɗanda ke da hannu a lamarin domin ɗaukar matakin da ya dace a kansu.