Masu garkuwa da mutane sun nemi a biya su Naira miliyan 20 kan kowane ɗan bautar ƙasa (NYSC) da aka sace kwanaki uku da suka gabata a jihar Kogi.
‘Yan NYSC ɗin na kan hanyarsu ne daga Bayelsa zuwa Abuja bayan kammala sansanin horaswa na makonni uku, lokacin da ‘yan bindigar suka tare motocinsu a kan titin Aloma-Egane a ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ya tabbatar da cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalan wanda abin ya shafa tare da neman N20m a matsayin kuɗin fansa.
Rundunar ‘yan sandan Kogi ta tabbatar da sace wasu fasinjoji, ciki har da ‘yan NYSC, inda ta ce an ceto mutum 11, ciki har da direbobin motocin biyu, bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka gudanar.
Sai dai har yanzu wasu daga cikin waɗanda aka sace suna hannun masu garkuwar. Iyalansu sun roƙi gwamnatin tarayya, hukumar NYSC da jami’an tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen ganin an kuɓutar da su cikin gaggawa.