Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiShugaban Hukumar Ƙidaya ta Najeriya ya rasu

Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Najeriya ya rasu

Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dr Aminu Yusuf Wushishi, ya rasu.

Rahotanni sun ce Dr Wushishi ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, watanni takwas kacal bayan ya fara jagorantar hukumar.

Marigayin ya karɓi ragamar shugabancin Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa a wani lokaci da hukumar ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da muhimman ayyukan ƙidaya da tattara bayanan jama’a.

An samu labarin rasuwarsa ne a yau, lamarin da ya jefa ma’aikata da abokan aikinsa cikin alhini.

Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya kuma ba iyalansa da ’yan uwansa haƙurin jure wannan babban rashi. Amin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments