Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiAn gano gawar wani ɗan acaba dan asalin jihar Kano da ya...

An gano gawar wani ɗan acaba dan asalin jihar Kano da ya ɓace a Abuja

An gano gawar wani ɗan kasuwar babur, Nura Yusuf, wanda aka dade ana neman sa, a cikin wani gini da ba a kammala ba a yankin Gas Pipeline da ke Unguwar Sabo-Tasha, a kan hanyar Abaji zuwa Gwagwalada a Abuja.

An gano gawar wani ɗan kasuwar babur, Nura Yusuf, wanda aka dade ana neman sa, a cikin wani gini da ba a kammala ba a yankin Gas Pipeline da ke Unguwar Sabo-Tasha, a kan hanyar Abaji zuwa Gwagwalada a Abuja.

Rahotanni sun ce Nura, ɗan asalin Bagwai da ke Jihar Kano, ya ɓace ne bayan ya ɗauki wasu fasinjoji zuwa yankin Gas Pipeline, inda ake zargin a shake shi har ya mutu.

Wani abokinsa, Ibrahim Baba, ya ce wasu manoma ne suka gano gawarsa a ranar Asabar bayan sun ji wani wari mai muni daga cikin ginin. Ya ce nan take suka sanar da ’yan sanda, waɗanda suka isa wurin suka tabbatar da mutuwar tasa.

Baba ya ce Nura ya shafe makonni yana bace, kuma tun bayan ɓacewarsa ba a sake samun damar kiran wayarsa ba. Ya ƙara da cewa marigayin, wanda ke zaune a garin Abaji, ya bar mata mai ciki.

Wani jami’in ’yan sanda daga sashen Abaji ya tabbatar da gano gawar, yana mai cewa saboda ta riga ta lalace sosai, an binne ta a wurin da aka gano ta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments