Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya karɓi rahotanni kan kadarorin da EFCC ta kwace

Tinubu ya karɓi rahotanni kan kadarorin da EFCC ta kwace

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi rahotanni daga Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, da Ministan Gidaje da Raya Birane, Muttaqha Rabe Darma, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Ganawar, wadda aka gudanar ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, ta mayar da hankali kan yadda za a gudanar da gidaje da kadarorin da EFCC ta kwace a sassa daban-daban na ƙasar.

An tattauna kan yadda za a tabbatar da cewa duk wani shiri na sayarwa ko rarraba kadarorin ya gudana cikin gaskiya, rikon amana da bin ƙa’idojin da suka dace.

Ofishin Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa ne ya bayyana hakan tare da fitar da hotunan ganawar.

Wannan na daga cikin ganawar da aka bayyana a bainar jama’a tsakanin Tinubu da Olukoyede tun bayan takaddamar da ta taso kan matakin EFCC na daskarar da asusun gwamnatin Jihar Osun, kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamnan jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments