An kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi a Jihar Bauchi ranar Litinin, 17 ga Agusta 2026.
Hukumar Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Bauchi (BASIEC) ta ce jam’iyyu 15 ne suka kammala shirye-shiryen shiga zaɓen.
Shugabar hukumar, Hajiya Jummai Salamatu Abubakar, ta bayyana hakan a Bauchi yayin da aka fara rabon kayayyakin zaɓe masu muhimmanci.
Ta ce za a kai kayayyakin ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro zuwa ƙananan hukumomi 20, sannan a rarraba su zuwa rumfunan zaɓe.
Jummai ta ce za a fara kaɗa ƙuri’a da ƙarfe 8 na safe, sannan a rufe rumfunan zaɓe da ƙarfe 3 na rana.
Ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a ƙananan hukumomi 19, yayin da zaɓen kansiloli zai gudana a dukkan ƙananan hukumomi 20.
Shira ce kaɗai ba za a gudanar da zaɓen shugabanta ba, saboda an riga an cike kujerar ta hanyar zaɓen cike gurbi.
A nasa bangaren, Sakataren Inter Party Advisory Council (IPAC), Khalid Arewa, ya ce jam’iyyun da za su shiga zaɓen sun gamsu da yadda shirye-shiryen ke gudana.
Ya ce suna da yakinin zaɓen zai kasance cikin gaskiya, adalci da zaman lafiya.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kuma ce ta tura jami’ai sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da tsaron masu zaɓe, jami’an zaɓe da kayayyakin zaɓe.
A wani mataki na daban, Gwamna Bala Mohammed ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutu a faɗin jihar.
Gwamnatin ta ce matakin zai bai wa ma’aikatan gwamnati damar shiga zaɓen ƙananan hukumomin da za a gudanar a jihar.