Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaTinubu na aiki ba dare ba rana domin cika alƙawuransa – Nentawe...

Tinubu na aiki ba dare ba rana domin cika alƙawuransa – Nentawe Yilwatda

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin ƙoshin lafiya da kuzari, yana aiki daga safe har zuwa dare domin aiwatar da manufofin gwamnatinsa da kuma cika alƙawuran da ya ɗauka wa ’yan Najeriya.

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, wanda ya yi ikirarin cewa Shugaba Tinubu ya gaji da jagorancin ƙasar.

A cewarsa, ikirarin cewa shugaban ƙasar ya gaji ba ya da tushe, domin Tinubu na ci gaba da halartar tarurruka, yanke muhimman shawarwari da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati a kullum.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a fannoni daban-daban, yana mai cewa sakamakon waɗannan matakai zai ƙara bayyana a nan gaba.

Shugaban APC na ƙasa ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai da goyon baya, yana mai jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen inganta tattalin arziki da rayuwar al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments