Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Peter Obi, ya bayyana cewa ba zai yi wa ‘yan Najeriya alkawarin samar da wutar lantarki na sa’o’i 24 cikin shekaru huɗu ba, yana mai cewa hakan ba abu ne mai yiwuwa ba.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce gina sabbin tashoshin samar da wutar lantarki da layukan isar da ita na buƙatar lokaci mai tsawo, don haka bai dace a yi alkawarin da ba za a iya cika ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa idan aka ba shi dama ya jagoranci ƙasar, gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan inganta samar da wutar lantarki, isar da ita da kuma rarraba ta yadda za a samu ingantaccen tsarin wutar lantarki a faɗin Najeriya.
Peter Obi ya ce gwamnatinsa za ta yi ƙoƙarin tabbatar da cewa ana samarwa, isarwa da kuma rarraba aƙalla megawatt 10,000 na wutar lantarki a kai a kai, yana mai cewa babban ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a yanzu shi ne tsarin isar da wutar da aka samar, ba wai samar da ita kaɗai ba.
Ya ƙara da cewa yana son gabatar da alkawuran da za a iya aiwatarwa maimakon ɗaukar alkawuran da ba su da tabbas, yana mai jaddada cewa gaskiya da aiki ne za su kasance ginshiƙin manufofinsa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.