Hamshakin attajirin Afirka, Aliko Dangote, na shirin bayar da kusan kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa domin ayyukan jin kai, kamar yadda ’yarsa, Halima Dangote, ta bayyana.
A cewarta, Dangote na da burin amfani da wani babban ɓangare na dukiyarsa, wadda aka kiyasta ta kai dala biliyan 35.1, wajen tallafa wa harkokin ilimi, lafiya, rage talauci da sauran ayyukan ci gaban al’umma.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinsa na mayar da wani ɓangare na arzikinsa ga jama’a ta hanyar ayyukan jin ƙai.