Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiMage ta shiga hannu bayan yunkurin fasa-ƙwaurin hodar iblis zuwa gidan yari...

Mage ta shiga hannu bayan yunkurin fasa-ƙwaurin hodar iblis zuwa gidan yari a Rasha

Hukumomin gidajen yari a Rasha sun kama wata mage da ake zargin an yi amfani da ita wajen fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi zuwa wani gidan gyaran hali da ke yankin Nizhny Novgorod.

Hukumomin gidajen yari a Rasha sun kama wata mage da ake zargin an yi amfani da ita wajen fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi zuwa wani gidan gyaran hali da ke yankin Nizhny Novgorod.

Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Yuli, lokacin da jami’an gidan yarin suka gano wata ƙwala da aka saƙa da hannu a jikin magen.

A cewar hukumomin, an ɓoye hodar iblis a cikin ƙwalar da aka ɗaura wa magen, lamarin da ya sa jami’ai suka kama dabbar tare da ƙwace miyagun ƙwayoyin.

Bayan an cire ƙwayoyin daga jikin magen, an duba lafiyarta domin tabbatar da cewa ba ta samu wata illa ba. Daga bisani, hukumomin sun sake ta.

Lamarin ya jawo hankali saboda yadda ake ƙoƙarin amfani da dabba wajen shigar da miyagun ƙwayoyi cikin gidan yari, duk da tsauraran matakan tsaro da ake amfani da su a wuraren gyaran hali.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments