Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMa’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce ta ƙi aminta da hadin gwiwa...

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce ta ƙi aminta da hadin gwiwa da hukumar bogi lokacin da ta nema

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa ta ƙi amincewa da buƙatar wata ‘majalisar bogi’ ta haɗa kai da ita, saboda ba ta da cikakken tushe na doka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa ta ƙi amincewa da buƙatar wata ‘majalisar bogi’ ta haɗa kai da ita, saboda ba ta da cikakken tushe na doka.

Ma’aikatar ta bayyana hakan ne a gaban kwamitin musamman na Majalisar Wakilai da ke binciken halaccin kafa, ayyuka da kuma shigar da Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) cikin kasafin kuɗin ƙasa.

A cewar ma’aikatar, hukumar ta taɓa neman haɗin gwiwa da ita, amma an ƙi amincewa da buƙatar saboda an gano cewa babu isasshiyar hujjar doka da ta tabbatar da kafa hukumar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da bincike kan yadda PFIPC ta samu damar bayyana a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, duk da tambayoyin da ake yi kan sahihancin kafuwarta da kuma ikon da take da shi na gudanar da ayyukan gwamnati.

Kwamitin Majalisar Wakilai ya gayyaci jami’an gwamnati da dama domin su bayyana rawar da suka taka wajen kafa hukumar, amincewa da ayyukanta da kuma shigar da ita cikin tsarin kasafin kuɗin ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments