Mafarauta tare da jami’an ƙungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kashe wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow a ƙaramar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce an kashe Kachalla Sani Yellow ne bayan musayar wuta da aka yi lokacin da mafarauta da jami’an CJTF suka dakile harin da wasu ‘yan bindiga suka kai.
Marigayin na daga cikin manyan shugabannin ‘yan bindiga da suka dade suna addabar ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru a jihar Zamfara.
Ana kuma zarginsa da kasancewa cikin jagororin ‘yan bindigar da suka shirya hare-hare kan al’ummomi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da kashe Kachalla Sani Yellow.
Bayan mutuwarsa, hotuna da bidiyon gawarsa sun bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ga an yi wa gunduwa-gunduwa da ita.