Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYadda jirgin yaƙin sojoji ya tarwatsa sansanin ’yan ta’adda

Yadda jirgin yaƙin sojoji ya tarwatsa sansanin ’yan ta’adda

Mataimakin shugaban makarantar Government Day Secondary School da ke Lassa a Ƙaramar Hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno, wanda ya kuɓuta daga hannun ’yan ta’adda, ya bayyana yadda zuwan jirgin yaƙin sojoji ya tilasta wa maharan tserewa, lamarin da ya ba su damar guduwa.

Ya ce maharan sun tsare su na tsawon kwanaki 98 a cikin daji, inda suka riƙa fuskantar matsanancin yunwa, wahala da azabtarwa. A cewarsa, suna cikin tsananin fargaba har sai da suka ji karar jirgin yaƙin sojoji, abin da ya sa ’yan ta’addan suka watse domin tserewa.

Ya bayyana cewa wannan ne ya ba su damar guduwa tare da wasu daga cikin mutanen da aka sace, kafin daga bisani dakarun soji suka ceto su tare da kai su wuri mai tsaro. Ya yabawa jami’an tsaro bisa rawar da suka taka wajen ceton rayuwarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments