Wasu ’yan bindiga sun kashe limamin wani kauye da wasu mutane uku tare da yin garkuwa da mazauna kauyen 12 a wani mummunan hari da suka kai kauyen Illela Dawagware da ke karamar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto.
Rahotannin da jaridar Daily Trust ta samu daga Sokoto sun ce wasu da ake masu garkuwar sun tafi da mazauna kauyen 12 a harin da suka kai kauyen Illela Dawagware da ke karamar hukumar Goronyo a Jihar Sokoto.