Akalla Falasdinawa huɗu sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata bayan wani hari da Isra’ila ta kai da sanyin safiyar Asabar kan wani gida da ke cikin Birnin Gaza, a cewar majiyoyin lafiya.
Kamfanin dillancin labarai na Wafa ya ruwaito cewa harin ya afkawa wani gida mallakin iyalan Al-Safadi da ke kan titin Al-Thalatheeni, lamarin da ya haddasa asarar rayuka tare da jikkata mutane da dama.
Jami’an agajin gaggawa sun garzaya wurin domin ceto waɗanda suka makale a ƙarƙashin baraguzan ginin tare da kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci domin samun kulawa.
Harin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin dakatar da hare-harren Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya.