Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Kano kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da gazawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwarzo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce matsalar tsaro a jihar Kano na ci gaba da ƙamari, tare da zargin cewa kashe-kashe, sace-sacen mutane da hare-hare a wasu yankuna sun ƙaru a cikin ‘yan kwanakin nan.
Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta sake duba dabarun da take amfani da su wajen tunkarar matsalolin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kariyar al’umma.
Sai dai gwamnatin jihar Kano ba ta fitar da wata amsa kai tsaye kan waɗannan zarge-zarge ba a lokacin da ake yada rahoton.