Jami’ar Bayero da ke Kano, BUK ta sanar da tsawaita lokacin neman rancen karatu na Nigerian Education Loan Fund, NELFUND ga ɗaliban da suka cancanta domin shekarar karatu ta 2025/2026.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa ta musamman da daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Lamara Garba, ya sanya wa hannu a madadin magatakardar jami’ar.
Garba ya ce an sake buɗe shafin neman rancen ne bayan buƙatar da mahukuntan jami’ar suka gabatar, domin bai wa ɗalibai damar neman rancen daga ranar 8 zuwa 29 ga Mayu.
Ya ce:
“Wannan sabon wa’adi shi ne dama ta ƙarshe ga ɗaliban da suka kammala tantancewa su shiga shafin NELFUND na hukuma domin fara da kammala neman kuɗin makaranta da na kula da kai.”
Ya kuma shawarci masu neman rancen da su bi duk matakan neman rancen yadda ya kamata tare da loda duk takardun da ake buƙata a shafin.
Garba ya jaddada cewa dole ne a loda dukkan takardu yadda ya dace domin kauce wa jinkiri ko rashin cancanta.
Ya ƙara da cewa neman kuɗin makaranta da na kula da kai dole ne a yi su lokaci guda, domin idan an raba su wataƙila ba za a duba su ba.
Haka kuma ya gargadi ɗalibai da kada su yi amfani da asusun wallet na bankunan microfinance kamar Opay da Moniepoint yayin neman rancen.
Ya ce ya kamata masu nema su tabbatar da cewa imel ɗinsu daidai ne kuma suna iya shiga cikinsa a kowane lokaci.
“Dole ne a adana kalmar sirri yadda ya kamata saboda za a riƙa amfani da ita wajen shiga shafin da bibiyar matsayin neman rancen,” in ji shi.
A ƙarshe, Garba ya buƙaci duk ɗaliban da suka cancanta su yi amfani da wannan dama ta ƙarshe kafin cikar wa’adin.