Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiƳan sanda sun kama wani mutum da sassan jikin ɗan adam a...

Ƴan sanda sun kama wani mutum da sassan jikin ɗan adam a Ogun

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 43 mai suna Idowu Ashafa, bisa zargin mallakar kan mutum da kuma tafin hannu guda biyu da aka ɓoye a cikin leda a yankin Igbesa na jihar.

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 43 mai suna Idowu Ashafa, bisa zargin mallakar kan mutum da kuma tafin hannu guda biyu da aka ɓoye a cikin leda a yankin Igbesa na jihar.

An kama shi ne yayin sintiri da jami’an ‘yan sanda ke yi da sassafe a ranar 17 ga Afrilu, 2026, karkashin jagorancin jami’an sashen Igbesa. Kakakin rundunar, DSP Oluseyi Babaseyi, ya bayyana cewa an tsayar da mutumin ne yayin sintirin da DPO CSP Solotan Owolabi ya jagoranta.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutumin ya tono gawar daga kabari a kauyen Ido Itekun da ke Igbesa, domin yin tsafi. Haka kuma, an gano kayan aikin da ake zargin ya yi amfani da su wajen aikata wannan laifi.

‘Yan sanda sun ce sun ziyarci wurin da abin ya faru domin yin bincike, sannan aka mika shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka, CID na jihar domin ci gaba da bincike.

Rundunar ta jaddada kudirinta na yaki da laifuka a jihar, tare da kira ga jama’a da su kasance masu lura da kai da kuma sanar da jami’an tsaro duk wani abu da ya sanya musu shakku.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments