Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane sama da 500 ake zargin sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren jiragen saman sojojin Najeriya da suka faru bisa kuskure cikin shekaru tara da suka gabata.
Wannan rahoto ya fito ne a daidai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce kan sabon harin da aka kai a kauyen Jilli da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda aka ruwaito mutuwar mutane da dama.
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa hare-haren sama da aka kai a baya sun yi sanadin mutuwar fararen hula, musamman a lokutan da sojoji ke kokarin kai hari kan ‘yan ta’adda amma sai hare-haren ya shafi jama’ar gari.
Masu sharhi da kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun nuna damuwa cewa irin wadannan hare-hare na kara jefa rayuwar fararen hula cikin hadari, musamman a yankunan da ‘yan ta’adda ke haduwa da jama’a ko kuma ke fakewa a cikinsu.
A cewar wasu rahotanni, daga shekarar 2017 zuwa yanzu, an samu hare-haren sama da dama da suka yi sanadin mutuwar mutane da yawa, lamarin da ke jawo tambayoyi kan ingancin bayanan sirri da ake amfani da su wajen kai hare-haren.
Sai dai hukumomin tsaro sun sha nanata cewa yawancin hare-haren ana kai su ne bisa sahihin bayanan sirri domin kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’adda, kodayake sun amincewa cewa wani lokaci ana iya samun asarar rayukan fararen hula.
Masana sun ce matsalar na da nasaba da yadda ‘yan ta’adda ke amfani da jama’a a matsayin kariya, abin da ke sa bambance tsakanin farar hula da ‘yan ta’adda ke zama abu mai wahala a irin wadannan yankuna.
Lamarin ya sake janyo kiraye-kirayen a kara inganta dabarun yaki da ta’addanci tare da kare rayukan fararen hula domin kauce wa irin wadannan munanan abubuwa a nan gaba.