Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiƘungiyar Izalawan Kwankwasiyya ta samu sabani da gwamnan Kano

Ƙungiyar Izalawan Kwankwasiyya ta samu sabani da gwamnan Kano

An samu rabuwar kai tsakanin ƙungiyar Izalawan Kwankwasiyya a Jihar Kano da gwamnatin jihar.

An samu rabuwar kai tsakanin ƙungiyar Izalawan Kwankwasiyya a Jihar Kano da gwamnatin jihar.

wannan dai na cikin sanarwar da mataimakin sakataren ƙungiyar Ustaz Isah Mika’il Muhammad ya fitar.

Sanarwar ta jaddada cewa sabinta shugabancin na zuwa ne bayan ficewar gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

Sabbin shugabannin sun hada da Malam Mus’ab Muhammad Tiga a matsayin shugaba na jiha, sai Ustaz Nasiru Yahaya Dan Agaji a matsayin mataimakin shugaban.

Sauran sun hada da Ustaz Aminu Ilyas a matsayin babban sakatare, Ustaz Isah Mika’il Muhammad a matsayin mataimakin sakatare, sai Malam Nazifi Dalhatu Dan Izala a matsayin jami’in hulda da jama’a na ɗaya.

Haka kuma akwai Ustaz Kabiru Sale a matsayin jami’in hulda da jama’a na biyu, ustaz Salisu Yaro Dan Gaske a matsayin daraktan kafafen sada zumunta, sai Malam Ridwan Sulaiman Zarewa a matsayin mataimakinsa.

A bangaren dattawa kuwa, an nada Malam Nuraddeen Haruna Yakasai a matsayin dattijo na daya, Malam Mustapha Kabiru Abdulmumin a matsayin na biyu, sai Alhaji Salisu Yahaya Bagobiri a matsayin na uku.

Haka kuma an nada Ustaza Fiddausi Yahaya Kofa a matsayin wakiliyar mata ta ɗaya, sai Ustaza Mariya Tukur Umar a matsayin wakiliyar mata ta biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments