Bayanai sun bayyana cewa dakarun gwamnati sun kai farmaki har na tsawon sa’o’i 7 kan tungar ƴan bindigar da ke yankin Tsafe, da ya yi ƙaurin suna sakamakon mahara da ke yin garkuwa da mutane a Zamfara.
Rahoton tsaro da mahukunta suke fitar a marecen jiya Lahadi, na cewa adadin ƴan bindigar da aka kashe ya kai 65, bayan da aka yi amfani da jiragen yaƙi da kuma sojin ƙasa domin afka wa ɓarayin dajin.
Majiyoyi dai sun nuna an kai hari ne a tungar magoya bayan ƙasungumin ɗan bindiga Ado Aleru, ya yin da wasu ke cewa daga cikin waɗanda aka hallaka har da ƴaƴa da kuma wasu zaratansa.
Ana dai kallon jihar Zamfara a matsayin matattarar masu garguwa da mutane a Najeriya, ya yin da sau da dama mahukunta ke sanar da ɗaukar matakai na musamman domin murƙushe ƴan bindigar amma hakan ya gagara.
Wani lokaci ma a shekarar da ta gabata, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ministan tsaro da babban kwamandan askarawan ƙasar umarnin da su tare a Sokoto, domin cafke ɗaya daga cikin jagororin ƴan bindigar, to amma har yanzu lamarin ya gagara.