Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiƘasa ta ruftowa masu harkarta a Kano, ana fargabar wasu sun...

Ƙasa ta ruftowa masu harkarta a Kano, ana fargabar wasu sun rasa ransu.

Ana fargabar cewa ma’aikatan yin tubali da dama sun rasa ransu bayan kasa ta bunne su a ramin da suke hako kasar da suke amfani da ita wajen yin tubali a ƙauyen Ridawa, ƙaramar hukumar Ghari a Jihar Kano, a ranar Laraba.

Ana fargabar cewa ma’aikatan yin tubali da dama sun rasa ransu bayan kasa ta bunne su a ramin da suke hako kasar da suke amfani da ita wajen yin tubali a ƙauyen Ridawa, ƙaramar hukumar Ghari a Jihar Kano, a ranar Laraba.

Lamarin ya faru ne yayin da ma’aikata ke haƙa rami mai zurfi domin samar da ƙasar yin tubali, inda kwatsam ramin ya rufta ya binne su.

Shaidu sun ce ruftawar ta jawo firgici a yankin, inda ma’aikata da mazauna gari suka garzaya domin fara ceton waɗanda abin ya shafa.

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ghari/Tsanyawa, Sani Bala, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa kimanin mutane 10 na iya kasancewa a ƙarƙashin ƙasa.

Ya buƙaci a kawo taimako cikin gaggawa daga hukumomi, musamman kayan aikin ceto na zamani domin tallafa wa aikin da ake yi.

Ya ce: “Muna buƙatar taimako cikin gaggawa domin ceton waɗanda har yanzu ke cikin ƙasa. Al’umma na ƙoƙari, amma ana buƙatar ƙwararrun kayan aikin ceto.”

A lokacin rubuta wannan rahoto, ana ci gaba da aikin ceto, inda mazauna gari da jami’an agaji ke tono ƙasa domin ceto waɗanda aka binne.
Sai dai har yanzu ba a ceto wasu daga cikin mutanen ba, lamarin da ke ƙara tsoron cewa adadin mace-macen na iya ƙaruwa.

Mazauna yankin sun ce irin waɗannan hatsarori na yawan faruwa a wuraren yin tubali na karkara, inda ma’aikata ke aiki a cikin ramuka masu zurfi ba tare da isassun matakan tsaro ko kulawa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments