Wakilin Ghana a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Yao Kumah, ya bukaci kasashe mambobin Majalisar da su goyi bayan kudirin da ke neman a amince da cinikn bayi ta tekun Atlantika a matsayin ‘laifi mafi girma ga bil’adama’, yana mai cewa hakan zai karfafa kokarin da ake yi na ganin an biyya diyya.
Matakin na da manufar neman goyon bayan kokarin bukatar a biya diyya ga ƴan Caribbean.
Kumah ya fada wa taron ‘yan jarida na Afirka kafin Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama ya kawo kudirin ga Babban Zauren Majalisar ranar Laraba cewa kudirin ba ya neman “kimanta shan wahala ko rage girman bala’o’in tarihi,” sai dai yana bayyana ‘muhimman gabobi na tarihi’ da suka sake fasalin mutumtaka da kafa tsarin da ke ci gaba da wanzar da rashin daidaito a duniya a yau.
“Tare da amincewa da wadannan al’amura na tarihi, kasashen duniya na kara karfafa ikonsu wajen magance kalubalen da ake fuskanta a yau wanda ya samo asali daga abubuwan da suka faru a baya,” in ji shi.
Kumah ya ce kudurin ya amince da fataucin mutane da kuma bautar da ‘yan Afirka a matsayin wani sabon rikici na tarihi wanda ya kawo nuna wariya a yadda ake juya duniya a yau