Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYan bindiga sun kai hari coci a jihar Kwara, tare da yin...

Yan bindiga sun kai hari coci a jihar Kwara, tare da yin awon gaba da masu ibada.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargi sun kai hari a wata cocin ECWA da ke ƙauyen Omugo a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, inda suka sace masu ibada da dama yayin gudanar da ibadar ranar Lahadi.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargi sun kai hari a wata cocin ECWA da ke ƙauyen Omugo a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, inda suka sace masu ibada da dama yayin gudanar da ibadar ranar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga cocin da safiyar Lahadi, suna harbe-harbe domin tsoratar da jama’a kafin su yi awon gaba da wasu daga cikin masu ibadar.

Ana zargin an sace kusan mutane tara, sai dai uku daga cikinsu sun samu ‘yanci bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai tare da haɗin gwiwar sojoji, ‘yan sanda, masu gadin daji da kuma ‘yan sa-kai.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran waɗanda aka sace, tare da farautar maharan da suka tsere zuwa cikin daji.

Lamarin ya haifar da fargaba a yankin, inda mazauna garin ke nuna damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ƙaruwa har ma suna kai farmaki a wuraren ibada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments