Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeKawo karshen yaki muke son ayi ba tsagaita wuta ba – Iran

Kawo karshen yaki muke son ayi ba tsagaita wuta ba – Iran

Iran ta sake nanata matsayarta na ƙin tsagaita wuta ba tare da kawo ƙarshen yaƙi ba.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta neman tsagaita wuta, sai dai tana maraba da kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya kuma na dindindin.

A yayin wata hira da ya yi da Al Jazeera a birnin Tehran, Araqchi ya ce: “Ba tsagaita wuta mu ke nema ba, domin ba ma son wannan yanayi ya sake maimaituwa nan gaba.

Muna son a kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya kuma na dindindin.”

Ya kuma zargi Amurka da shiga yaƙin bisa ƙarfafawar Isra’ila in da ya ce,

“A yau waɗanda suka nemi mu miƙa wuya ba tare da sharaɗi ba, su ne ke neman taimakon abokan hamayyarsu domin buɗe mashigar Hormuz,”.

Dangane da lafiyar jagoran addinin ƙasar, Mojtaba Khamenei, Araqchi ya ce: “Gwargwadon abin da na sani, raunin da ya samu sama-sama ne, kuma yana cikin koshin lafiya, yana kuma da cikakken iko kan al’amura.”

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments