Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiYaƙin Amurka, Isra'ila da Iran ya girgiza kasuwar man fetur ta duniya

Yaƙin Amurka, Isra’ila da Iran ya girgiza kasuwar man fetur ta duniya

Yaƙin da ke gudana kan Iran ya kawo tashin hankali a kasuwar makamashi ta duniya.

Yaƙin dake ci gaba da gudana tsakanin Amurka da Isra’ila kan Iran, ya janyo gagarumin koma baya a kasuwannin makamashi na duniya, yayin da ƙasar da ke yankin Gabas ta Tsakiya ta kasance guda daga cikin manyan ƙasashen da ke samar da ɗanyen mai a duniya.

Tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran ne Tehran ta kulle mashigin Hormuz wanda ta nan ne ake gudanar da hada-hadar mai ta duniya baki ɗaya.

Tun bayan barkewar rikicin ne dai farashin danyen mai ya haura dala 80 kan kowace ganga sakamakon fargabar katsewar samar da mai daga yankin.

Tuni dai Iran ta rufe mashigar ruwa ta Hormuz, wadda ita ce babbar hanya ga kashi daya bisa biyar na man fetur din da duniya ke samu.

Kasancewar Iran ita ce kasa ta biyar a duniya wajen arzikin mai, tana fitar da kusan ganga miliyan hudu a kowace rana, kuma hare-haren soji na iya lalata cibiyoyin hakar mai da matatun kasar.

Tashin farashin man fetur a duniya wani al’amari ne da ke taka rawa wajen haifar da tsadar rayuwa la’akari da cewa lamuran da suka shafi rayuwar yau da kullum na gudana ne tare da gudun mowar makamashi.

Shigar Amurka da sauran kasashen Yamma cikin rikicin ya kara rura wutar fargaba ga masu zuba jari a fannin makamashi, wanda ke ci gaba da jefa kasuwar cikin rashin tabbas.

Masana na cewa, idan har ba a yi gaggawar neman mafita kan wannan rikici ba, to kuwa yanayin kasuwar makamashi zai ci gaba da kasancewa cikin ha’u’la’i.

SourceFRI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments