Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin jihar Sokoto ta barranta kanta kan bai wa ƴar TikTok mota

Gwamnatin jihar Sokoto ta barranta kanta kan bai wa ƴar TikTok mota

Gwamnan Jihar Sokoto ya musanta maganar bai wa yar TIKTOK Rahama mota

Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin gwamna Ahmed Aliyu ta musanta labaran da ke cewa gwamnan na da hannu wajen bai wa wata ƴar tiktok kyautar mota.

A cikin wata sanarwa da daraktan harkokin yaɗa labarai na gwamnan jihar, Abubakar Bawa ya fitar, ya ce “ofishinsa na son tsame Gwamna Ahmed Aliyu daga batun bayar da kyautar, domin ba ta da wata alaƙa kowace iri da gwamnan”.

A ƙarshen mako nan ne dai wani bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna wasu maza biyu na miƙa kyautar mota ga wata sananniyar ƴar tiktok a birnin Sokoto ya haifar da muhawara.

Mutanen biyu sun yi iƙirarin cewa sun ba ta motar ce a matsayin kyautatawa sanadiyyar “soyayyar” da take yi wa gwamnan jihar.

Sai dai lamarin ya janyo suka daga wasu masu amfani da shafukan sada zumunta, waɗanda suka yi zargin cewa an yi ‘amfani ne da kuɗin’ gwamnati yin kyautar.

Source BBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments