Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi ƙarin haske kan gyaran dokar zaɓe ta 2022 da majalisar ta amince da ita a makon da ya wuce.
Amincewa da gyare-gyare ga dokar ya bar baya da ƙura, inda ƴan adawa da ƙungiyoyi suka riƙa sukar majalisar kan rashin amincewa da gyaran sashen da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura.
A lokacin da ya yi jawabi a wurin ƙaddamar da wani littafi a Abuja a ranar Asabar, Godswill Akpabio ya ce ba a yi watsi da tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba, sai dai an cire wurin da aka ce tura sakamakon zaɓen “ka-tsaye”.
Ya ƙara da cewa:
“Abin da kawai muka ce shi ne a cire ɓangaren da ya ce ‘kai-tsaye’, domin idan aka ce haka to akwai batun matsalar ‘network’ inda ba za a iya tura saƙo ba.
Da dama na ganin cewa tura sakamakon zaɓe kai-tsaye zai rage maguɗin zaɓe da ake zargin ana a lokutan zaɓe a faɗin ƙasar.