Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba da wasu za su rika fitowa suna cewa ga wanda zai yi takara ba saboda a cewarsa hakan zai sake haifar da rarrabuwar kai a jam’iyyarsu ta APC.
Tun da fari dai wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC ne a Kano suka amince da cewa sanata Barau Jibrin, shi ne zai yi takarar gwamna a jihar a 2027.
Ga alama dai wannan dambarwa ta ayyana sanata Barau Jibrin, a matsayin wanda wa su ke so ya yi wa jam’iyyar APC takarar gwamnan jihar na ci gaba da daukar hankali, musamman bayan da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya takawa maso fitowa suna nuna goyon baya ga wani mutum daya birki.