Dan wasan Bayern Munich da tawagar Ingila, Harry Kane, ya sadaukar da nasarar lashe kyautar Ballon d’Or ta 2026 ga matarsa, Katie Goodland, wadda ta halarci bikin bayar da kyautar a birnin Landan.
Kane ya bayyana matarsa a matsayin babban mai mara masa baya, inda ya ce nasarar ba tasa kadai ba ce, ta iyalinsa ce baki daya. Ya kuma gode mata bisa sadaukarwar da take yi domin taimaka masa cimma burinsa.
An ga Katie Goodland cikin farin ciki da motsin rai yayin da mijinta ke karbar kyautar, bayan ya doke manyan ‘yan wasa ciki har da Kylian Mbappé da Lamine Yamal.
Wannan nasara ta sanya Kane zama dan Ingila na farko da ya lashe kyautar Ballon d’Or cikin shekaru 25, tun bayan Michael Owen a shekarar 2001.