Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa yankin Arewa zai ƙara yawan ƙuri’un da zai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, idan aka kwatanta da zaɓen 2023.
Shettima ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin ƙaddamar da sabon ofishin ƙungiyar Arewa for Asiwaju, wadda ke goyon bayan sake zaɓen Tinubu, a birnin Abuja.
Ya yi iƙirarin cewa Arewa ta ba Tinubu kashi 60.2 cikin 100 na ƙuri’un da ya samu a zaɓen 2023, yana mai cewa yana da yaƙinin cewa yankin zai ƙara yawan ƙuri’un da zai ba shi a zaɓe mai zuwa.
Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci shugabannin siyasa a yankin Arewa da su haɗa kai wajen tallafa wa Tinubu, domin tabbatar da nasararsa a zaɓen 2027.
A cewarsa, Arewa ba ta da dalilin fargaba game da yunƙurin Tinubu na neman wa’adi na biyu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sai dai ikirarin Shettima game da yawan ƙuri’un da Arewa za ta bai wa Tinubu a zaɓen 2027 ra’ayinsa ne, kuma sakamakon zaɓen ne zai tabbatar da yadda masu zaɓe za su yi zaɓinsu.