Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiADC-PCC ya yi Allah-wadai da dakile taron ‘yan “Tinubu Must Go” a...

ADC-PCC ya yi Allah-wadai da dakile taron ‘yan “Tinubu Must Go” a Kano

Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da dakile taron “Tinubu Must Go” da aka shirya gudanarwa a The Avenue Event Center da ke Kano, tana mai cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da dakile taron “Tinubu Must Go” da aka shirya gudanarwa a The Avenue Event Center da ke Kano, tana mai cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na majalisar, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Lahadi, jam’iyyar ta zargi ’yan sanda da take haƙƙin yin taro cikin lumana da faɗin albarkacin baki.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun toshe ƙofar wurin taron, tare da hana taron ƙarƙashin jagorancin Lauya Abba Hikima. ADC ta kuma nuna damuwa kan rahoton kama mamallakin cibiyar taron.

Jam’iyyar ta zargi gwamnatin APC da amfani da ’yan sanda wajen danne masu ra’ayin adawa, tana mai cewa ya kamata a mayar da hankali kan rashin tsaro, ayyukan ’yan bindiga da tsadar rayuwa.

ADC-PCC ta buƙaci a saki mamallakin wurin taron ba tare da wani sharaɗi ba, idan yana hannun jami’an tsaro. Ta kuma yi kira ga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da su sanya ido kan lamarin, tana mai jaddada cewa yin zanga-zanga cikin lumana haƙƙi ne na kundin tsarin mulki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments