An zargi rundunar ’yan sandan jihar Kano da hana masu gangamin ‘Tinubu Must Go’ gudanar da taronsu a jihar, lamarin da ya jawo suka daga jagororin ƙungiyar.
Ɗaya daga cikin jagororin gangamin, Abba Hikima Fagge, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga magoya bayan ƙungiyar.
Abba Hikima, wanda lauya ne, ya zargi Kwamishinan ’Yan Sandan Kano da tura jami’an tsaro domin rufe wurin da aka tanada don gudanar da taron.
Ya bayyana matakin a matsayin rashin adalci da kuma keta dokokin ƙasa, tare da zargin cewa ana nuna son kai wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Haka kuma, ya yi kira ga rundunar ’yan sandan da ta guji abin da ya kira kare muradun jam’iyyar APC, yana mai cewa ya kamata jami’an tsaro su gudanar da aikinsu ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar Kano ba ta fitar da sanarwar hukuma kan zarge-zargen da aka yi mata ba.