Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTsohon kyaftin din Super Eagles Troost-Ekong ya karɓi Musulunci a Qatar

Tsohon kyaftin din Super Eagles Troost-Ekong ya karɓi Musulunci a Qatar

Tsohon kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong, ya karɓi addinin Musulunci bayan ya furta kalmomin Shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar.

Tsohon kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong, ya karɓi addinin Musulunci bayan ya furta kalmomin Shahada a birnin Doha na ƙasar Qatar.

Rahotannin kafafen yaɗa labarai na Qatar sun ce ɗan wasan mai shekaru 33 ya bayyana karɓar Musuluncin ne yayin da yake Doha, inda a yanzu yake taka leda a ƙungiyar Al-Ahli. Bidiyon da ke nuna Troost-Ekong yana furta Shahada ya kuma yaɗu a kafafen sada zumunta.

Troost-Ekong ya buga wa Najeriya wasanni 83 tsakanin 2015 da 2025, inda ya kasance kyaftin din Super Eagles a lokuta daban-daban. A gasar AFCON ta 2023, ya jagoranci Najeriya zuwa wasan ƙarshe sannan aka zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan wasan gasar.

Ya sanar da yin ritaya daga buga wa Super Eagles a shekarar 2025, bayan ya shafe kusan shekaru goma yana wakiltar Najeriya. Rahotannin da suka bayyana karɓar Musuluncinsa ba su kawo bayani kan abin da ya sa ya ɗauki wannan mataki ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments