Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu ta bude shafin raba wa yan Najeriya tallafin N50,000

Gwamnatin Tinubu ta bude shafin raba wa yan Najeriya tallafin N50,000

Hukumar Bunƙasa Ƙananan da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN) ta sake buɗe shirin tallafin kuɗi na N50,000 ga ƙananan ‘yan kasuwa a faɗin ƙasar, domin taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu da faɗaɗa harkokin kasuwanci.

Tallafin, wanda ba rance ba ne, ba ya buƙatar a mayar da kuɗin.

Sai dai, hukumar ta gindaya sharadin cewa duk wanda ya amfana da shirin dole ne ya ɗauki aƙalla mutum ɗaya aiki.

Hukumar ta bayyana cewa za a iya amfani da kuɗin wajen sayen kayan aiki, ƙara jari, inganta sana’a da faɗaɗa kasuwanci.

Ta kuma buƙaci masu neman tallafin su cike fom ɗin neman tallafin tare da bayar da sahihan bayanansu, ciki har da sunan kasuwanci, lambar waya da nau’in sana’ar da suke gudanarwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments