Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya sanya dokar hana zirga-zirga ta tsawon sa’o’i 24 a Minna, babban birnin jihar, sakamakon tashin hankalin da aka samu a wasu sassan birnin.
Dokar za ta fara aiki nan take bayan an kammala sallar Juma’a, kuma za ta ci gaba da aiki har sai gwamnati ta ba da wata sanarwa.
Gwamnatin jihar ta umarci mazauna Minna da su zauna a gidajensu, tare da kauce wa duk wani zirga-zirgar da ba dole ba a lokacin dokar.
Haka kuma, an umarci jami’an tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar, tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin birnin.
Matakin ya biyo bayan zanga-zanga da tashin hankali da aka samu a a yau dangane da mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne, waɗanda rahotanni suka ce sun mutu ne a hannun jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Minna.
Gwamnatin jihar ta shawarci mazauna garin da su kwantar da hankalinsu, su zauna a gidajensu, tare da bin umarnin jami’an tsaro.
Ana sa ran gwamnatin Neja za ta fitar da ƙarin bayani yayin da ake ci gaba da bibiyar halin da ake ciki.