Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiCBN ta ƙara tsaurara sa ido kan tallafa wa ƴan ta'adda da...

CBN ta ƙara tsaurara sa ido kan tallafa wa ƴan ta’adda da kuɗi

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ɗauki sa ido kan harkokin samar da kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci a matsayin ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da yake bai wa fifiko a yanzu, domin kare tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasar daga amfani da shi wajen ayyukan haramtattu.

A cikin wata sanarwa da Mukaddashiyar Daraktar Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari na CBN, Hakama Sidi-Alli, ta sanya wa hannu, bankin ya ce ƙarin sa ido zai mayar da hankali kan haɗarin tallafa wa ta’addanci, sa ido kan hada-hadar kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci, aiwatar da takunkuman kuɗi da aka tanada, da kuma bayar da rahoton hada-hadar kuɗi da ake zargin tana da alaƙa da tallafa wa ta’addanci.”

CBN ya ce zai ci gaba da amfani da wani muhimmin tsari wanda ya haɗa da sa ido ta hanyar ziyartar cibiyoyi da kuma sa ido daga nesa, domin ƙarfafa matakan yaƙi da halatta kuɗaɗen haram, dakile tallafa wa ta’addanci da kuma dakile samar da kuɗaɗen yaɗa makamai masu hatsarin gaske (AML/CFT/CPF) a fadin ɓangaren kuɗi.

A cewar babban bankin, za a aiwatar da wannan tsarin sa ido ne “bisa tanade-tanaden dokoki da ƙa’idojin da ake da su.”

CBN ya ce wannan matakin sa ido zai kuma taimaka wa Najeriya wajen ci gaba da haɗin gwiwar cikin gida da na ƙasa da ƙasa wajen yaƙi da tallafa wa ta’addanci da kuɗi, dakile samar da kuɗaɗen yaɗa makamai masu hatsarin gaske, da tabbatar da ingancin tsarin kuɗi tare da kare tsarin hada-hadar kuɗin ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments