Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamna Idris ya rushe kwamitin hukumar zaɓen jihar Kebbi

Gwamna Idris ya rushe kwamitin hukumar zaɓen jihar Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya rushe kwamitin gudanarwa na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi (KEBSIEC).

An bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da Daraktan Majalisar Zartarwa, Kabiru Hassan Wasagu, ya fitar, wadda Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya sanya wa hannu. An rabawa ’yan jarida wasiƙar a Birnin Kebbi ranar Talata.

Sanarwar ta ce: “An umarce ni da sanar da ku cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya amince da rushe kwamitin gudanarwa na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi, sakamakon cikar wa’adin aikinsa, kuma matakin zai fara aiki daga ranar 18 ga Satumba, 2026.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa sauran mambobin hukumar guda biyu da wa’adinsu bai ƙare ba za su ci gaba da kasancewa a kan muƙamansu har sai an sake kafa hukumar.

Gwamnan ya yaba wa mambobin da wa’adinsu ya ƙare bisa hidimar da suka yi wa jihar, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ta ƙara ƙudurin kare ’yancin kai da mutuncin hukumar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments