Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai gudanar da Hawan Maulidi a cikin birnin Kano, a wani sabon salo da ake cewa shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan hawa a tarihin Masarautar Kano.
Wasu majiyoyi a fadar Sarkin sun shaida wa Daily Nigerian Hausa cewa za a gudanar da hawan ne a ranakun Asabar da Lahadi, inda Sarkin zai fito domin shiga cikin bukukuwan Maulidin Annabi Muhammad (SAW).
Majiyoyin sun ce shirin na daga cikin hanyoyin nuna soyayya da girmamawa ga Manzon Allah (SAW), tare da fito da wasu daga cikin al’adun da suka shafi bukukuwan Maulidi a Kano.
A wasu masarautun Arewacin Najeriya, ana gudanar da irin wannan hawa a ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal a matsayin wani ɓangare na bukukuwan Maulidi.
Ana sa ran Hawan Maulidin zai ƙara jawo hankalin jama’a tare da nuna yadda al’ummar Kano ke gudanar da bukukuwan Maulidi cikin salo na musamman.
Kano ta daɗe tana shahara wajen gudanar da bukukuwan Maulidi, musamman tarukan zikiri, wa’azi da sauran shirye-shiryen tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW).