Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce mulkin jihar Kano ba abu ne mai sauƙi ba, saboda yawan jama’arta da kuma kasancewarta jiha mai cike da al’ummomi daga sassa daban-daban na Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, wanda ya wakilce shi a taron tsaro na shekara-shekara na Institute of Security and Strategic Studies.
Yusuf ya kwatanta Kano da “ƙaramar Najeriya”, yana mai cewa mutane daga sassa daban-daban na ƙasar suna zaune a jihar, lamarin da ke ƙara wahalar gudanar da mulkinta.
Ya ce gwamnatinsa na amfani da hanyoyin magance matsalar tsaro na soja da kuma na farar hula, ciki har da horas da matasa kusan 2,000 na Neighbourhood Watch tare da tura su ƙananan hukumomi 44.
Gwamnatin ta kuma kafa Anti-Phone Snatching Corps da shirin Safe Corridor, wanda aka ce an yi shi domin ƙarfafa matasan da ke da hannu a daba da tashin hankali su ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.
A cewar Waiya, matasa kusan 340 ne aka yi wa rajista da tantancewa ƙarƙashin shirin Safe Corridor, yayin da gwamnati ta ware sama da Naira miliyan 500 domin gudanar da shirin.
A nasa jawabin, masanin tsaro, Dr Muhammad Ali, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma su ƙara haɗin gwiwa wajen yaƙi da ’yan bindiga, garkuwa da mutane, satar shanu, haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da sauran laifuka.
Ali ya kuma ba da shawarar ƙarfafa musayar bayanan sirri, sintiri na haɗin gwiwa a kan iyakoki da kuma haɗa kan jami’an tsaro da al’ummomin yankin domin dakile matsalar tsaro.