Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiIBB: Masu hannu da shuni sun taimaka wajen nasarar juyin mulkin soji

IBB: Masu hannu da shuni sun taimaka wajen nasarar juyin mulkin soji

Tsohon shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce wasu attajirai fararen hula sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa juyin mulkin soji da aka yi a Najeriya.

Tsohon shugaban mulkin soji, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce wasu attajirai fararen hula sun taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa juyin mulkin soji da aka yi a Najeriya.

Babangida ya bayyana hakan ne a wata hira da Badeggi 90.1 FM da ke Minna, yayin da ake bikin cika shekarunsa 85.

Ya ce babu wani juyin mulkin soji da ya yi nasara a tarihin Najeriya ba tare da taimakon fararen hula ba.

Babangida ya kuma sake magana kan kisan tsohon abokinsa, Janar Mamman Vatsa, wanda aka zarga da hannu a wani yunkurin juyin mulki a shekarar 1985.

Ya ce da farko ya yi wahala ya yarda da zargin saboda tsawon dangantakarsu, tun daga lokacin da suke makaranta tare a Bida har zuwa shiga aikin soja.

A cewarsa, an kafa kwamitin bincike bayan an samu rahotannin da ke alakanta Vatsa da Janar Mohammed Gado Nasko da yunkurin kifar da gwamnatinsa.

Ya ce kwamitin ya wanke Nasko, amma ya gano shaidun da suka danganta Vatsa da shirin juyin mulkin.

Babangida ya ce abin ya matuƙar ba shi haushi, amma ba shi da ikon sauya hukuncin da dokar soji ta tanada ga wanda aka samu da irin wannan laifi.

An harbe Vatsa a watan Maris na 1986 bayan da aka same shi da hannu a yunkurin juyin mulkin.

Babangida, wanda ya karɓi mulki a juyin mulkin watan Agustan 1985, ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu fata tare da bai wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya.

Ya ce yana da yakinin matakan da gwamnati ke ɗauka za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki da tsaro da ƙasar ke fuskanta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments