Wani ginin da ake a yankin Dandishe, Kwanar Yashi, da ke ƙaramar hukumar Fagge a Jihar Kano, ya ruguje, inda mutane 16 suka samu raunuka.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, yana mai cewa an samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 4:32 na asuba.
Ya ce jami’an hukumar sun garzaya wurin nan take, inda suka tarar da wani gini mai girman ƙafa 20 zuwa 30 ya ruguje gaba ɗaya. Jami’an sun samu nasarar ceto mutane 13, ciki har da yara, daga cikin baraguzan ginin.
Daga cikin waɗanda aka ceto akwai Al-Mustapha Yusuf mai shekaru 15, Khadija Yusuf mai shekaru 7, Ummusalama Yusuf mai shekaru 10, Madina Yusuf mai shekaru 6 da Hafsat Yusuf mai shekaru 9. Wasu uku, Affan Yusuf mai shekaru 5, Hassana Yusuf mai shekaru 7 da Ummulkursum Yusuf mai watanni tara, an ceto su cikin sume.
An miƙa dukkan waɗanda abin ya shafa ga Usman Ibrahim, wani ɗan uwan mahaifinsu, domin kai su asibiti don ƙarin kulawar lafiya. Hukumar kashe gobarar ta ce ana gudanar da bincike domin gano musabbabin rushewar ginin, tare da shawartar mazauna jihar su ƙara taka-tsantsan a lokacin damina domin kauce wa irin waɗannan hadurran.