Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiTsohon minista Dalung ya soki waƙar Rarara kan Pantami

Tsohon minista Dalung ya soki waƙar Rarara kan Pantami

Wata sabuwar waƙar siyasa da fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, ya fitar tana sukar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ta jawo ce-ce-ku-ce da suka mai da hankali kan mawaƙin maimakon wanda ake suka. Masu sharhi da dama sun ce maimakon waƙar ta rage wa Pantami farin jini, sai ta ƙara masa goyon baya da tausayin jama’a.

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya soki salon waƙar, yana cewa siyasar Arewa ta saba amfani da waƙoƙi wajen wayar da kai da ilmantarwa, ba cin mutunci da yaɗa zarge-zarge ba. Ya ce idan akwai abin da ake zargin Pantami da shi, ya kamata a gabatar da hujjoji maimakon kai hare-haren da suka shafi mutunci.

Sauran masu sharhi da masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana cewa amfani da zarge-zargen da ba a tabbatar da su ba ba ya gina siyasa mai tsafta, illa yana lalata martabar tattaunawar siyasa. Wasu kuma sun yi gargadin cewa irin wannan salo na iya cutar da ɗan takarar da ake ƙoƙarin tallatawa fiye da wanda ake kai wa hari.

Masu sharhi sun yi kira ga ‘yan siyasa da masu waƙoƙin siyasa su rungumi ladabi da girmama juna, suna mai cewa bambancin ra’ayi bai kamata ya zama dalilin cin mutunci ko yaɗa zarge-zarge ba. Sun jaddada cewa siyasa za ta wuce, amma kyawawan ɗabi’u da mutunta juna su ne za su ci gaba da dorewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments