Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yaba wa shugabannin Kungiyar Limaman Katolika ta Najeriya (CBCN) bisa yadda suka bayyana wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu halin da ƙasar ke ciki ba tare da tsoro ba.
Sani ya ce jawabin da limaman suka gabatar wa shugaban ƙasa ya nuna jajircewa wajen faɗar gaskiya ga masu mulki, yana mai cewa shugabannin addinai suna da alhakin tunatar da gwamnati halin da jama’a ke ciki da kuma ba da shawara idan akwai buƙata.
Ya bayyana cewa a cikin dimokuraɗiyya, irin waɗannan bayanai masu cike da gaskiya da shawara suna taimakawa wajen inganta shugabanci da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga gwamnati.
Tsohon sanatan ya kuma yi kira ga gwamnati da ta karɓi irin waɗannan shawarwari da zuciya ɗaya, tare da ɗaukar matakan da za su rage wahalhalun rayuwa da inganta tattalin arziki da tsaro.
Shehu Sani ya jaddada cewa faɗar gaskiya ga masu mulki ba adawa ba ce, illa wata muhimmiyar hanya ce ta ƙarfafa dimokuraɗiyya, tabbatar da gaskiya da kuma taimakawa gwamnati wajen magance matsalolin da ke addabar ƙasa.